Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Hausa Ta Duniya: Hausawa Sun Taimaka Wajen Kwato 'Yancin Ghana - John Mahama


Ranar Hausa Ta Duniya
Ranar Hausa Ta Duniya

Tsohon shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya ce Hausawa sun taka rawar gani da bai misaltuwa a fafutukar yakin neman ‘yancin kasar ta Ghana. Ya kara da cewa, al’adun sojin Ghana sun kasance cike da ta Hausawa tun kafin a kafa Ghana.

Tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama da yake jawabi a wajen taron bukin ya ce, “Al'ummar Hausawa sun ba da gudummawa kwarai wajen ci gaban kasarmu tun daga lokacin da aka fara shiri har zuwa lokacin haihuwar kasarmu Ghana. Hausawa sun taka rawar gani mara misaltuwa a yakin neman yancin kasar Ghana”.

Tsohon Shugaba John Dramani Mahama ke jawabi a Ranar Hausa Ta Duniya
Tsohon Shugaba John Dramani Mahama ke jawabi a Ranar Hausa Ta Duniya

Ya kara da cewa, dakarun soji sun yi amfani da harshen Hausa kwarai wajen maci a lokacin Gold Coast, kafin Ghana ta samu ‘yancin kai.

Bukin Ranar Hausa ta Duniya na burin hada kan al’ummar Hausawa a duk inda suke a fadin duniya tare da yada al’adun gargajiyarsu. Bukin wannan rana a birnin Accra ya tabbatar da hakan, domin an baje kolin al’adun Malam Bahaushe inda ‘yan tauri, da masu rawar koroso, da mahaya dawakai suka kayatar da filin taron.

Wasanni da raye rayen gargajiya
Wasanni da raye rayen gargajiya

Wasu da suka halarci wajen da Muryar Amurka ta ji ra’ayinsu game da bukin wannan shekarar, kamar sarkin Anya kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar sarakunan zangon Ghana, Alhaji Jibril Sissy, da shugaban kungiyar hadin kan Hausawan duniya, Mohammed A. da magajiyar sarkin Hausawan Nima, Hajiya Azumi Ibrahim sun bayyana farin cikinsu da bukin wannan shekarar, musamman jawabin da tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama, ya yi matukar kayatar da su.

Wasanni da raye rayen gargajiya
Wasanni da raye rayen gargajiya
Tsohon shugaban kasa, John Mahama bai kammala jawabinsa ba sai da ya dan taba Hausawa, domin kamar yadda ya ce akwai wasa tsakanin kabilarsa ta Gwanjawa da Hausawa. Ya ba da wani labari na barkwanci na yadda wani limami Bahaushe, wanda ya fito daga Najeriya, ya jagoranci sallah ba da alwala ba; abokan wasan nasa da sauran jama'a su ka barke da dariya da anashuwa bayan jin wannan kagaggen labari na tabo abokan wasan nasa.

Jama'a dai sun bayyana farin cikinsu da bukin wannan shekarar, musamman jawabin da tsohon shugaban kasa, John Dramani Mahama, ya yi matukar kayatar da su.

Mata ma ba a bar su a baya ba
Mata ma ba a bar su a baya ba

Saurari cikakken rahoton Idris Abdallah Bako:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG