Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gaza Biyan Albashi Zalunci Ne-inji Malam Adamu Ciroma


Masallaci kusa da Abuja
Masallaci kusa da Abuja

A jawabin da ya yi a wurin rufe tafsirin bana a Abuja tsohon ministan kudi Malama Adamu Ciroma ya yi mamakin yadda gwamnonin Najeriya ke gaza biyan albashin ma'aikatansu

Malam Adamu Ciroma ya kwatanta gaza biyan albashi da zalunci.

Adamu Ciroma yace idan ya tuna aikin gwamnati a zamanin mulkin turawan Ingila ya kan yi juyayin zamanin yau. Yace yana mamaki cewa wadanda gwamnatocin kasar nan suka kirasu suka basu aiki, suna aiki akan sharadin za'a biyasu wata wata sai gashi yau ma'aikacin gwamnati zai yi wata da watanni ba'a biyashi ba. Yace gaza biyan albashi zalunci ne kuma ba'a iya gina gwamnati ta gari akan zalunci.

Dangane da sabon shugaban kasar Najeriya yace suna yi mashi addu'a Allah ya bashi nasarar yin aiki nagari. Yace shugaban ya basu tabbacin cewa aikinsa na farko shi ne kawar da zalunci da kawar da Boko Haram da makamantansu. Yace idan ko za'a fara aikin gyara to a fara da gida, wato ma'aikatan gwamnati. A tabbata an biyasu lokacin da ya kamata a biyasu albashinsu.

Shi ma mai gabatar da tafsirin Shaikh Husseini Zakariya ya bukaci gwamnatin Buhari kada ta juya baya kan soke shingayen bincike na sojoji. Yace sau da yawa akan dauki marasa lafiya daga Keffi zuwa Abuja amma sai su mutu a hanya saboda tsananain tafiyar hawainiya akan hanya sanadiyar shingaye a kan hanya. Sau da yawa an sha haifar jajrirai cikin motoci. Wasu masu haihuwan sukan mutu a hanya saboda babu likita don ba'a samu an kaisu asibiti ba. Ya roki gwamnati ta kare jama'a daga wahalar da suke sha kan hanya zuwa Abuja da kuma irin wulakancin da ake yi masu.

Shaikh Sirajo Na Alhaji Sabo Keffi ya gargadi jama'a kada su yi garaje wajen neman canji daga gwamnatin Buhari. Yace a yi masu addu'a domin barnar shekara da shekaru da aka yi ana yi zata dauki lokaci kafin a kawar da ita.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Gaza Biyan Ma'aikata Albashi Zalunci Ne-inji Malam Adamu Ciroma - 2'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG