Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Kano Mai Jiran Gado Abba Yusuf, Zai Duba Batun Tsige Sarkin Kano Na 14, Muhammadu Sanusi - Kwankwaso


Dr. Rabiu Kwankwaso
Dr. Rabiu Kwankwaso

Kwankwaso ya kasance mai kakkausar suka kan matakin da gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ya dauka na tsige Sarki Sanusi daga mulki a watan Maris na 2020

Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a zaben 2023, ya bayyana cewa gwamnan jihar Kano mai jiran gado Abba Yusuf, zai duba batun tsige Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da ya fitar ranar Asabar.

Tsohon gwamnan jihar Kano din, shi ne wanda wa’adinsa na karshe ya kai ga hawar Sanusi karagar Mulki sakamakon rasuwar Sarki a wancan lokaci, wato Alhaji Ado Bayero.

Kwankwaso ya kasance mai kakkausar suka kan matakin da gwamna mai barin gado Abdullahi Ganduje ya dauka na tsige Sarki Sanusi daga mulki a watan Maris na 2020.

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano
Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Ganduje ya kuma raba masarautar Kano gida biyar tare da nada sabbin sarakuna.

Daga nan ne aka kori Sanusi daga Kano aka tura shi garin Loko, wani yanki mai nisa a jihar Nasarawa, yayin da aka fara gudanar da bincike kan kudaden da masarautar ta kashe a karkashin jagorancinsa.

Kwankwaso, wanda jam’iyyarsa ta NNPP ta gudanar da yakin neman zabe bisa tsarin kawo sauyi da shugabanci na gari, ya sha alwashin hada kai da gwamnati mai jiran gado domin shawo kan matsalolin da suka shafi tsige Sanusi da kuma rarrabuwar kawuna da masarautar Kano ta yi.

Ya bayyana cewa, a matsayinsu na dattawa, za su ci gaba da bai wa gwamnati shawarar yin abin da ya dace.

Gwamna Rochas Okorocha, da Gwamna Rabiu Kwankwaso tare da Sarki Sanusi a fadar gwamnatin Jihar Kano.
Gwamna Rochas Okorocha, da Gwamna Rabiu Kwankwaso tare da Sarki Sanusi a fadar gwamnatin Jihar Kano.

Kwankwaso ya kara da cewa, “Wadanda aka bai wa wannan dama za su zauna su duba lamarin. Mai daki shi yasan inda yake masa zuba, Za su duba abin da ya dace su yi a halin da suka sami kansu. Bayan tsige Sarki, hatta Masarautar ta rabu gida biyar. Duk waɗannan suna buƙatar sai anzo an yi nazari. Galibi shugaba yakan gaji abubuwa masu kyau da kuma abubuwa masu wahalar warwarewa”.

Tsohon gwamnan ya bayyana fatansa cewa Allah ya shiga tsakani kuma ya bai wa gwamnati mai jiran gado damar gudanar da al’amuran jihar yadda ya kamata.

Batun tsige Sanusi da kuma raba masarautar Kano ya kasance batutuwan da suka jawo cece-kuce a ciki da wajen kasar.

Kiraye-kirayen da Kwankwaso ya yi na sake duba lamarin da gwamnati mai jiran gado ta yi kan iya haifar da muhawara da batutuwa a cikin kwanaki masu zuwa.

XS
SM
MD
LG