Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An nada Jega A Matsayin Shugaban Jami'ar Sa'adatu Rimi


Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, Farfesa Attahiru Jega.
Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na Najeriya, Farfesa Attahiru Jega.

Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta amince da nada tsohon shugaban hukumar zabe ta Najeriya INEC, Farfesa Muhammad Attahiru Jega a matsayin uba ga sabuwar Jami’ar nazarin koyar da aikin malinta ta Kano, wato Sa’adatu Rimi University of Education, Kumbotso.

Kazalika Gwamnatin ta Kano, ta amince da nada Oba Dr. Moshood Olalekan Ishola Balogun Aliiwo a matsayin shugaban majalisar kula da ayyukan Jami’ar.

Gabanin zama shugaban hukumar zabe ta Najeriya INEC, Farfesa Attahiru Jega ya shugabanci Jami’ar Bayero Kano tsawon shekaru biyar, haka kuma kafin haka, ya kwashe shekaru da dama yana koyar da ilimin kimiyyar siyasa a Jami’ar ta Bayero.

Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega a Abuja, Maris 30, 2015.
Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega a Abuja, Maris 30, 2015.

Kwamishinan labaru na gwamnatin Kano Malam Mohammed Garba wanda ya sanar da haka bayan zaman majalisar zartarwa ta jihar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranta a jiya lahadi, yace a kwanan nan ne hukumar kula da Jami’o’I ta Najeriya wato NUC ta amince da daga likafar kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, wato Sa’adatu Rimi College of education zuwa matsayin Jami’ar nazarin koyon aikin malinta wato University Of Education.

Kwamishinan yace sauran mambobin majalisar kula da ayyukan sabuwar Jami’ar sun hada da Dr. Muhammad Adamu Kwankwaso da Hajiya Zulaiha U.M Ahmed da Dr. Ibrahim Yakubu Wunti Dr. Halima Muhammad da kuma Alhaji Sabiu Bako.

Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega a wajen taron manema labarai
Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega a wajen taron manema labarai

A cewar Kwamishinan, Majalisar zartarwar ta Kano ta amince da nada shugabannin da zasu tafiyar da ayyukan Jami’ar na yau da kullum, wadanda suka hada da Farfesa Isa Yahaya Bunkure a matsayin shugaban Jami’ar da Kabiru Ahmed Gwarzo mataimakin shugaba mai kula da al’amuran karatu da Dr. Miswaru Bello mataimakin shugaba mai kula da harkokin mulki sai kuma Saminu Bello babban magatakarda na Jami’ar.

Sauran sune Hajiya Mabruka Abubakar Abba shugabar sashin kula da dakunan karatu na Jami’ar yayin da aka nada Ibrahim Muhammad Yahaya babban Jami’in kula da al’amuran kudade.

Ita dai sabuwar Jami’ar nazari da koyon aikin Malinta ta Sa’adatu Rimi dake Kano, ita ce ta 61 a jerin Jami’o’I Mallakar Jihohi yayin da ta kasance ta 222 a jerin Jami’o’in Najeriya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG