Fiye da yara dari da talatin ne a sansanin ‘yan gudun hijira, da basu tare da iyayensu biyo bayan hare-haren da ‘yan Boko Haram suka kai arewacin jihar Adamawa.
Jami’in hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA, mai kula da sansanonin ‘yan gudun hijira dake Yola Alhaji Sa’adu Bello, ne shedawa wakilin muryar Amurka, Ibrahim Abdulazeez, a sansanin dake Yola.
Ya kara da cewa hukumar nada shirin na masamman na kula da irin wadannan yara, wanda ya hada da mikasu ga hannu nagari domin kula dasu.
Hukumar shige da fice ta kasa ita ma ta dukufa wajen wayar wa jama’a kan dangane da masu mugun nufi da kan fake akan iyakar kasar.
Mr. Obekpekanu, shugaban hukumar shige da fice, a jihar Adamawa, yace hukumar sa da jami’an tsaro na gudanar da wasu aiyukan sirri da zai taimaka wajen bankado mabuyar masu kai hare-haren.