A zahirance kimanin kananan hukumomi gomasha uku ne har yanzu suke karkashin kulawar ‘yan kungiyar boko haram, a jihohin Borno, Yobe da Adamawa. Wannan ya na haddasa dar-dar ga hukumomi da jama’a dangane da gudanar da zabe a wadannan kanan hukumomin. Ta bakin masana harkar tsaro na ganin wannan wani abun damuwane, a cewar Dr. Bawa Abdullahi Wase, yana ganin idan har ba a dauki kwararan matakai ba to za’a kai lokacin da kasar ma za’a wayi gari bata, ganin yadda abubuwa ke kaiwa da kawowa. Ya yi kari da cewar idan har ana bukatar magance wannan matsalar kafin lokacin zabe to da akwai bukatar ayi abu uku, wanda yace abu na farko shie a samar da kayan aiki ga dakaru mayakan Najeriya, abu na biyu kuwa shine, a tabbatar da cewar an fito da duk ilahirin dakarun Najeriya daga cikin barikoki wadan da basa aikin komai illa shan farfesu, kana kuma abu na uku shine, a tabbatar da cewar an fayyace gaskia wadan da ake ganin kamar suke makarkashiya a tsakanin shuwagabani, su fito su bayyana ma duniya gaskiya wadannan abubuwan sune zasu taimaka a kai ga gaci.
A ganin wani masani Dr. Amoga Keptin Namala, malami a jami’ar Modibbo Adama da ke Yola, yace yana ganin idan har gwamnati bata dauki matakan da suka kamata ba to wannan zai iya kawo cikas a harkokin zabe bama a wadannan kanana hukumomin ba kawai, harma a yanki na Arewa maso gabas baki daya. Yayi nuni da cewar wannan ya nuna gwamnati ta gaza, wanda hakin shugaban kasane ya kare al’uma kasar, amma ya bayyana cewar ita gwamnati babban damuwar ta shine yazatayi ta cimma burinta.
Wasu kungiyoyi na kokarin wayar da kan al’uma dangane da yaki da ta’addanci, ga ta bakin wani shugaban wata kungiya me kokarin wayar da kan al’umah dangane da siyasa da yaki da ta’addanci a Najeriya Alh. Usman Usman Fulani, yace wannan kungiyar an kafata ne don a wayar ma Fulani kai dangane da yadda zasu shiga siyasa kuma suyi zaben da ya dace dasu, kuma kada su bari ayi amfani da su wajen bangar siyasa ko wani aiki na batagari.