Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bata Gari Sun Kai Hari Gidan Dan Takarar Gwamnan Gombe a Karkashin APC


APC
APC

Yayin da 'yan takara ke kara kaimi a neman kuri'u wasu 'yan ta'ada kuma sun soma kai hari a kansu.

'Yan ta'adan sun kaddamar da kai hare-hare kan 'yan siyasa.

Hari na baya bayan nan shi ne wanda wasu 'yan bata gari suka kai kan gidan dan takarar neman kujerar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam'iyyar APC, Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya. Shi ma gwamnan mai ci yanzu Ibrahim Hassan Dankwambo wasu 'yan bata gari sun kai masa farmaki yayin da ya ziyarci garin Kashere.

Sabili da ire-iren wadannan lamuran ya sa rundunar 'yansandan jihar Gombe ta bakin kakakinta DSP Fwaji Attajiri ta ja kunnuwan 'yan siyasa a jihar da su kauracewa duk wani abun da ka iya tada zaune tsaye. Yace kwamishanansu ya kira 'yan siyasa ya gargadesu suyi siyasa cikin lumana. Kada wani ya je ya bata kayan wani domin yin hakan ya sabawa dokar kasa kuma 'yansanda zasu kamashi su gurfanar dashi gaban kuliya.

Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya dan takaran ya gana da manema labarai ya kuma bayyana masu abun da ya faru dashi. Yace yana ganawa da mutanensa a gidansa 'yan ta'ada suka shigo gidan suka kawo hari. Wadanda suka yi kokarin kaishi wurin jam'an tsaro sai da aka sassaresu. Sun kuma fasa motocin dake kofar gidansa. Sun kai rahoton abun da ya faru wurin 'yansanda.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG