A ci gaba da kokarin wayar ma Jama’a kai game da sha’anin tsaro, rundunar ‘yan sanda ta Najeriya tare da hadin gwiwar kamfanin ayyukan tsaro na ABAM dake Kano, sun shirya taron lacca ga limamai da ‘yan kasuwa da kuma Jami’an kananan hukumomi a Kano.
Wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari wanda ya aiko ma na da rahoton, ya ruwaito Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyyar Kano, wadda ta kunshi Kano da Jigawa da Katsina, na cewa makasudin shirya wannan batir shi ne a ankarar da jama’a cewa harkar tsaro ba ta jami’an tsaro ma ne kawai. Har ma da su kansu jama’a. To amma y ace lallai mutane na bayar da hadin kai sosai musamma a Kano saboda su kan bai wa jami’an tsaro bayan sirri da kan taimaka sosai.
Shugaban kamfanin tsaron na ABAM, wanda ya shirya taron da hadin gwiwar hukumar ‘yan sanda, Keftin Abdullahi Bakoji Adamu ya ce sun ba da muhimmanci ga ‘yan kasuwa ne saboda ganin yadda ake ta auna su a hare-hare. Ya ce maharan sun fai kai hare-haren ne a wuraren da jama’a ke da yawa irin kasuwanni da sauransu. Ya ce baya ga ‘yan kasuwar ma sun kuma gayyaci jami’an kananan hukumomi don su ma su je su fadakar da jama’arsu.
Abdul Mudallabi Isa Daneji, wani daga cikin ‘yan kasuwar da su ka halarci taron, ya ce lallai taron zai amfane su gaya.