Gwamnan jihar Borno Kashin Shattima Ibrahim, ya bayyanar da cewar gwamnatin shi na iya bakin kokarinta ta ga cewar an samu zaman lafiya a jihar da ma kasar baki daya, ganin yadda zabe ya karato yanzu damuwar su shine yaza’ayi a gudanar da zabe a jihar batare da wani damuwaba.
Yace wannan tashe tashen hankullan ba zasu sa akiyin zabe a wadannan yankin ba, ganin cewar anyi zabe a wasu kasashe da ke fama da yake yake, amma duk da haka ba a ki yin zabeba, kamar su Abganistan, Libya, Irak da dai sauransu don haka maganar zabe hakin ‘yan Najeriya ne wadanna da ke a gida da waje.
Don haka babu wani dalili da zai sa a hanama yan kasa suyi zaben a bun da suke so ba bisa ga wannan dalilin babu wata hujja da zata sa a hanamusu zabe. Yace babban damuwar shi yanzu shine yaza’ayi a samu zaman lafia a yankisu su taimakama al'uma, ba wai maganar zabe ba, wanda yasan da cewar idan da rai da lafiya to zabe zai gudana a yanki wanda yanzu abun da yarage zuwa ga zabe kwanaki kadan ne, don haka babu wanda ke da tabbas ko ze kai lakacin zaben.