Shugaban Turkiyya Recep Tayyib Erdogan ya ce wadanda su ka shirya juyin mulkin bara, wanda bai yi nasara ba, maciya amanar kasa ne wadanda ya kamata a fille masu kai.
Erdogan ya yi wannan kalamin ne yayin da kasar ke shagulgulan zagayowar ranar ta wajen ayyana ranar hutu, inda ya kafa wani abin tuna wadanda ya kira 'shahidai' a kan shahararriyar gadar nan ta Bosporus da ke birnin Istanbul don girmama mutane kimanin 250 da su ka mutu wajen kokarin hana juyin mulkin. Gadar, wadada ake sake ma suna zuwa Gadar Shahidai a jiya Asabar, anan ne aka yi arangama tsakanin farar hula da sojoji masu tafe da tankokin yaki.
A wani jawabin da ya yi daga bisani, Erdogan ya ce wadanda su ka shirya juyin mulkin sun cancanci kisa ko kuma jefawa gidan yari makamancin Guantanamo Bay na Amurka. Ya ce muddun Majalisar Dokokin Turkiyya ta amince da dokar kashe wadanda su ka yi juyin mulkin to labudda zai rattaba hannu akai.
"Sun nuna rashin tausayi lokacin da su ka auna bindigoginsu kan jama'a ta," a cewar Erdogan, wanda ya kara da cewa, "Me kuma mutane na ke dauke da su? -- ba komai sai tutocin da su ka rike - kamar dai yadda su ka yi yau -- sannan sai kuma wani abu wanda ya fi muhimmanci, wato imani."
Facebook Forum