Tsohon gwamnan jihar Jigawa a Najeriya, Alhaji Sule Lamido ya ce lokacin sulhu ya yi a tsakanin ‘ya’yan jam’iyar PDP mai adawa bayan hukuncin da kotu ta yanke a tsakiyar makon nan, wanda ya bayyana Sanata Ahmed Makarfi a matsayin halartaccen shugaban jam’iyar.
“Wannan hukuncin ba wanda ya fadi babu wanda ya ji kunya, babu wanda za a yi wa shagube ko zolaya.” In ji Lamido, yayin wata hira da ya yi da Sashen Hausa na Muryar Amurka.
A ranar Larabar da ta gabata ne kotun koli dake Abuja ta bayyana kwamitin da Makarfi ke jagoranta a matsayin bangaren dake da hurumin shugabantar jam’iyar wacce ta sha kaye a zaben 2015.
Ana sa ran hukuncin zai kawo karshen rudanin shugabanci da jam’iyar ta kwashe kusan shekaru uku tana fama da shi tun bayan da ta fadi a zaben.
“Jam’iyar PDP ce ta ci nasara, ba wai makarfi ya ci ba ko Sheriff ya fadi ba, PDP ce ta ci nasara.” Tsohon gwamnan na Jigawa wanda jigo ne a jam'iyar ta PDP ya fadawa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari.
Mutane da dama yanzu sun zuba ido ne su ga iya gudun jam’iyar, tunda kusan za a iya cewa ta tsallake tsiradi na farko.
“Mu a PDP yanzu shi ne mu ga cewa yaya aka yi wadannan abubuwa suka faru, sannan mu zo mu yi sulhu ya mu ya mu… domin tunkarar zabe na gaba.”
Jam’iyar ta PDP ta fada cikin rudani ne tun bayan da tsohon shugabanta Ahmed Mu’azu ya ajiye shugabancin jam’iyar bayan da ya fuskanci matsin lamba kan kayen da suka sha a hanun APC mai mulki.
Ita dai PDP ta kwashe sama da shekaru 16 tana mulkar Najeriya.
Saurari cikakkiyar hirar ta Alhaji Sule Lamido da wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari:
Facebook Forum