Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FIFA Ta Dakatar Da Shugaban FECAFOOT Samuel Eto'o Tsawon Watanni 6


FILES-FBL-ESP-CMR
FILES-FBL-ESP-CMR

An samu tsohon dan wasan Bercelona da laifin keta dokokin FIFA dangane da “munanan dabi’u na saba ka’idojin yin adalci ga kowa da rashin da’a daga ‘yan wasa ko masu horaswa”.

Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta haramtawa Samuel Eto’o shiga harkokin wasanni tsawon watanni 6 saboda wasu halaye daya nuna yayin gasar kwallon kafar mata ‘yan kasa da shekaru 20.

Tuhume-tuhumen nada nasaba da wasan Kamaru na zagaye na biyu tsakaninta da Brazil, inda kasar ta kudancin Amurka ta samu nasara da ci 3-1 bayan karin lokaci.

An baiwa Eto’o da tawagar kasar Kamaru jan kati akan bugun daga kai sai mai tsaron ragar daya baiwa Brazil damar farke kwallon da aka zura mata a wasan da suka buga a birnin Bagota, na kasar Colombia a ranar 11 ga watan Satumbar daya gabata.

An dakatar da Eto’o daga halartar wasannin Kamaru, na ajin maza ko mata, saidai dakatarwar bata shafi matsayinsa na shugabancin hukumar kwallon kafar Kamaru ta FECAFOOT ba.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG