Sheik Halluru Maraya daya ne daga cikin manyan malaman addini musulunchi a Kaduna, kuma ya ce kamata ya yi gwamnati ta yi dokoki kan satar mutane ba wa'azi ba.
Ita ma kungiyar Kiristochi ta Nigeriya CAN ta ce hukuncin ya yi mata daidai. Rev. Joseph John Hayap shine shugaban kungiyar a Kaduna, ya ce tun farko suma sun yi niyar shigar da ‘kara amma lauyansu ya ce ‘kara ‘daya da aka shigar ya isa.
To sai dai mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna ka harkokin addinin musulunci, Sheik Jamil Abubakar Albani, ya ce akwai kuskuren fahimta game da wannan doka, kasancewa har yanzu ba ta kai ga mai girma gwanan jihar Kaduna ba, kafin ya yi nazarinta domin matakin da zai ‘dauka.
Dama dai tun bayan kai wannan kudurin dokar wa'azi gaban Majalissar Dokokin Kaduna a shekarar 2016, darikar Fentacostal ta shigar da kara gaban babar kotun Kaduna wanda a ranar Laraba nan alkaliyar kotun mai Shari'a Hannatu Gwadah ta yanke hukuncin cewa kudurin ya sabawa kundin dokar kasa na 1999.
Domin Karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.
Facebook Forum