Mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro, Baba Gana Monguno, shi ne ya sanarwa manema labarai da wannan batu, jim kadan bayan kammala wani babban taro a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis 20 ga watan Yuni.
Wannan lamari ya ja hankalin majalisar kula da malaman makarantun allo a jihar Kaduna dake gani matakin da ake shirin dauka bai dace ba.
Imam Buhari Maraban Jos, sakataren majalisar malaman makarantun allo a jihar Kaduna, ya ce sun yi mamakin jin wannan sanarwar akan almajirai daga mutumin da ya fito daga Maiduguri. Ya kuma ce kamata yayi idan an hango wata matsala a zauna da shugabannin kungiyarsu ta kasa a ga yadda za a magance matsalar.
Imam Buhari, ya kuma ce mafi yawan wadanda ake gani akan titi suna bara, ba almajirai bane, rashin shugabanci na gari ne ya haifar da wannan matsalar har wasu ke amfani da rigar almajirai su na bara.
Shi kuma mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna akan harkokin addinin musulunci Sheikh Jamilu Abubakar Albani, ya ce ko da yake akwai kurakurai game da almajirci a Najeriya, bai kamata a yanke wannan hukuncin ba tare da an tattauna da malaman dake wannan harka ba, a ji yadda suke gani ya fi dacewa a magance matsalar.
Masanin harkokin tsaro Manjo Yahaya Shinko mai ritaya, shi kuma ya ce a ganin sa, rashin tsaro bai da alaka da almajiranci amma dai da bukatar a gyara batun karatun Muhammadiyya a kasar.
Ga karin bayani cikin sauti daga Isah Lawal Ikara.
Facebook Forum