An sami jerin fashe fashe uku daya bayan daya, a Mumbai babban birnin kasuwancin India, akalla mutane 21 suka halaka, da jikkata wasu fiyeda dari, a lamari da hukumomin kasar suka kira “harin ta’addanci da aka shirya.”
Fashe fashen sun auku ne a wasu sassan birnin a yammacin yau, a wurare da ke cike makil da mutane, biyun daga cikin fashe fashen sun auku ne kudancin birnin, daya kuma a tsakiyar Mumbai. Sakatare na musaman mai kula da tsaron cikin gidan kasar, U.K. Bansal, yace da alamun wan nan harin ta’adanci ne da aka shirya da nufin halaka rayuka.
Babu wani da ya fito ya dauki alhakin kai harin nan da nan. Hukumomin kasar suna bincike. Wan nan shine harin mafi muni, tun bayan kawanya da mayakan sakai dake da gindin zama a Pakistan suka kai wa birnin hari a 2008 suka kashe mutane 166.
Pakistan bata bata lokaci ba wajen yin Allah wadai da harin na yau.