Tsohon kwamandan sojojin Sabiyawan Bosniya Rafko Mladic ya yi ta gayawa alkalan dake sake sauraron karar da ake tuhumarshi da aikata laifukan yaki bakaken maganganu yau Litinin, ya kuma ki amsawa ko musanta laifuka goma sha daya da ake zarginsa da aikatawa, daga nan aka tilasta mashi ficewa daga kotun dake birnin Hague. Bayan da aka umarci dogarawar Majalisar Dinkin Duniya su fitar da Mladic daga kotun, alkali Alphons Orie ta musanta aikata laifin a madadin tsohon sojan Bosniyan dan shekaru 69. Wannan ne karo na biyu da mutumin da ake zargi da yiwa Musulmi dubu takwas da kananan yara kisan kare dangi a Srebrenica, bayyana gaban kotun. Wannan ne kisan gilla mafi muni a tarihin kasar turai tun bayan karshen yakin duniya na biyu. Mladic da aka kama a watan Mayu bayan ya shafe shekaru 16 yana buya, ya yi barazanar kauracewa sauraron karar sabili da har yanzu jami’an kotun basu amince da lauyoyin da yake so su kare shi ba. Amma duk da haka ya bayyana gaban kotun ya kuma yi ta sa baki yayinda Orie ke magana. Lokacin da alkalin ya tambaye shi ko a shirye yake ya saurari laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa sai ya cewa alkalin yayi abinda ya ga dama. Amma da zarar alkalin ya fara karanta laifukan da ake tuhumarsa a kai sai Mladic ya ce’ “a,a, kada ka karanta mani, kada ka kara magana.” Orie ya sa aka fitar da Mladic yayinda ya ci gaba da hanawa a karanta laifukan da ake zarginshi da aikatawa.
Tsohon kwamandan sojojin Sabiyawan Bosniya Rafko Mladic ya yi ta gayawa alkalan dake sake sauraron karar da ake tuhumarshi da aikata laifukan yaki bakaken maganganu yau Litinin, ya kuma ki amsawa ko musanta laifuka goma sha daya da ake zarginsa da aikatawa,