Mata 'yan wasan kwallon kafar kasar Japan sun lashe kofin duniya na shekarar bana ta 2011 sun yi galaba a kan 'yan wasan Amurka a bugun penariti bayan wasan karin lokacin da ya biyo bayan kunnen dokin da su ka yi biyu da biyu.
Nasarar ta jiya lahadi ta sa Japan ta zama ta farkon da ta lashe kofin duniya a nahiyar Asiya, kuma wadda ta hana Amurka samun kofin a karo na ukku. 'Yan wasan Amurka sun lashe kofin duniyar a shekarar 1991 da kuma shekarar 1999.
A gasar ta bana wadda kungiyar FIFA ta wasan kwallon kafa ta duniya ta shirya an kai kungiyar 'yan wasan kwallon kafar Amurka wani matsayi na can kololuwa, ta yadda ita ce babbar mowar da kowa ya baiwa nasara a wasannin karshen da aka yi a Frankfurt, kasar Jamus.
Ranar lahadin makon jiya Amurka ta kai ga wasannin kusa da na karshe bayan wata nasarar ba zato akan 'yan wasan Brazil, sannan kuma ranar laraba Amurka ta doke 'yan wasan Faransa ta kai ga wasannin karshe.
Japan kuma ta kai ga wasannin karshe ne bayan ta doke 'yan wasan Sweden a ranar laraba. A wasan kusa da na kusa da na karshe Japan ta yi nasara akan 'yan wasan kasar Jamus masu masaukin baki.