Dubban mutanen dake zanga zangar neman garambawul a tsarin zaben kasar Malashiya sun gamu da tankiyar gaske daga ‘yan sanda a Kuala Lumpur, wadanda suka yi amfani da mesar ruwa da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar. Yan sanda a babban birnin kasar sun ce an kama sama da mutane dubu daya da dari hudu yau asabar, ana kuma kyautata zaton sakin akasarinsu cikin ‘yan sa’oi masu zuwa. Jam’iyun hamayya sun ce an kama wadansu shugabannin yayinda aka jiwa a kalla shugaban hamayya daya kananan raunuka. Da dama daga cikin masu zanga zangar sun yi take suna cewa, “Allah ja zamanin al’ummar kasar”, suna kuma dauke da balo mai ruwan dorowa da kuma furanni. Yan sanda sun killace titunan birnin Kuala Lumpur da dama domin ya zama da wuya magoya bayan ‘yan hamayyar su isa babban filin wasan kasar inda suke niyar taruwa. Gamayyar kungiyoyin da suka shirya gamgamin sun ce kimanin mutane dubu hamsin duka shiga zanga zangar da aka gudanar yau asabar, sai dai ‘yan sanda sun musanta haka da cewa kimanin mutane dubu shida ne suka halarta. Kamfanin dillancin labarai na AP dake wurin yayi kiyasin cewa, tsakanin mutane dubu 20 da dubu 30 suka halarci gangamin.
Yansandan kasar Malashiya sun yi arangama da masu zanga zanga suka kuma kama sama da mutane 1,400
Dubban mutanen dake zanga zangar neman garambawul a tsarin zaben kasar Malashiya sun gamu da tankiyar gaske daga ‘yan sanda a Kuala Lumpur, wadanda suka yi amfani da mesar ruwa da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar.