Jami’an kula da zirga-zirgar jiragen ruwa na kasar Girka sun ce ‘yan fashi sun cafke wani jirgin ruwan tanka na kasar a dab da gabar Najeriya.
Jami’ai sun fada yau litinin cewa a ranar asabar aka yi fashin jirgin dakon man fetur mai suna "Aegean Star" da ma’aikatansa su 20. Suka ce an yi fashin wannan tanka a cikin teku kimanin kilomita 55 daga gabar Najeriya a cikin mashigin ruwan Guinea, a lokacin da yake kan hanyar zuwa Jamhuriyar Benin dauke da mai daga kasar Ghana.
An ce ma’aikatan jirgin ruwan sun hada da Girkawa uku da wasu daga kasashe dabam-dabam. Har yanzu babu labarin halin da suke ciki.
Koda yake ba su yi kaurin suna kamar takwarorinsu na Somaliya ba, ‘yan fashi cikin teku su na kara zafafa ayyukansu a cikin mashigin ruwan Guinea. A watan da ya shige, Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Jiragen Ruwa ta Duniya ta ja kunnen jiragen ruwa game da wucewa ta kusa da jamhuriyar Benin. Hukumar ta ce ‘yan fashi sun kwace jiragen ruwa da dama a wannan shekara, ciki har da wani jirgin ruwan tanka na Girka da aka yi fashinsa ranar 16 ga watan Yuni.