Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: A Gujewa Tashin Hankali -inji Matasan APC


Gangamin APC
Gangamin APC

Matasan jam'iyyar APC a jihar Filato sun yi taron jawa kansu kunnuwa akan su gujewa tashin hankali lokacin zabe da bayan an gama.

Matasan sun ce sun gaji da yadda 'yan siyasa ke anfani da addini da kabilanci wajen haddasa rikici tsakanin al'umma.

Shugaban matasan ya bayyana makasudin shirya taron. Jeremiah Mareng daya daga cikin shugabanin matasan yace suna neman canji amma da zaman lafiya domin irin wurare kamar su Maiduguri babu zaman lafiya. Ko a Filato an samu rashin zaman lafiya. Yace amma su matasan sun gane cewa wasu ne suke anfani dasu domin su cimma burinsu. Yace babu wanda ya kamata su goya ma baya sai Janar Buhari.

Wani Adamu Jeji yace yana tabbatarwa duniya cewa da ikon Allah APC ce zata kafa sabuwar gwamnati ta kuma kawo canji. Idan sun kafa gwamnati a Filato suna da abubuwan da zasu tanadawa matasa domin su daina tada hankali.

Mahalarta taron sun hada da matasan musulmi da na kirista daga unguwanni daban daban wadanda a da can basa ko ga maciji da juna. Wani yace da sun fuskanci matsaloli da dama amma yanzu kawunansu sun waye. Yanzu sun hada kai kuma ba zasu bari a kawo masu banbancin addini ko na bangaranci ba.

Ga rahoton Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG