Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Danyen Mai Ya Tashi A Duniya


A jiya Laraba farashin danyen mai ya tashi, biyo bayan rahottanin da aka bada masu cewa Kungiyar kasashe masu arzikin mai suka cimma matsayar yawan man da suke hakowa.

Idan kuwa har suka rage din, wannan ne zai zama karo na farko da kungiyar ta tsayar da irin wannan shawara a cikin shekaru takwas.

Ba a bayyana tushen wa’yannan labaran ba dake cewar kasashen OPEC din zasu rage kadan ne a cikin abin da suke samarwa, daga ganguna miliyon 33 zuwa ganguna milyan 32 da dubu dari biyar a duk rana. Kungiyar OPEC dai take samr da sulusi daya na dukkan man da ake sha a duniya.

farashin mai ya taba haura dollar dari ganga guda, amma daga bisani sai ya rika fadiwa musamman a shekarar 2014 inda samar da mai ya inganta ayyuka a Amurka.

A da, idan aka samu fadiwar parashin mai, kasashen OPEC suna daukar shawarar rage samar da mai wanda ke haifar da tashin parashin. Saudi Arabia dake taka muhimmiyar rawa a harkar OPEC itace tafi hanzari wajen saurin rage man da take sarrafawa.

Amma a ‘yan kwannakin nan hukumomin na Saudiya sun ce ba zasu kara rage mansu ba har sai sauran kasashen dake cikin OPEC su kuma sun biyo sawu, sun rage nasu man, abinda yassa yawan man ya ci gaba da karuwa a kasuwanni amma farashinsa na ci gaba da foduwa warwas a kasa.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG