Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iran Zata Dau Mataki Kan Masu Zanga Zanga


Masu zanga zanga
Masu zanga zanga

Magoya bayan gwamnatin Iran sun gudanar da wani gagarumin gangami a yau Juma’a a fadin Iran, yayin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke shirye shiryen kiran taron gaggawa domin tattaunawa akan zaman dar dar a kasar.

Dubban masu goyon bayan gwamnatin Iran ne suka gudanar da gangamin kwanaki uku a jere a wurare da dama a cikin Tehran da sauran Birane bayan babban jagoran kasar Ali Khamenei ya bukaci hukumomin kasar da su dauki mataki kwakwkwara akan wadanda suke da hannu wajen tada zaune tsaye da aka kwashe mako ana gudanar da gangamin kin jinin gwamnati.

Wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 22 da kuma kame dubbai a sauran wurare. Jami’an Iran sun ce wannan shirin hukumar leken asirin Amurka ta CIA ne, tare da Isra’ila da ma Saudi Arabiya, wadanda sune suke da alhakin barkewar tashe-tashen hankula kan makwabtan kasar Iran tun daga nasarar da Donald Trump yayi ta zabe.

Babban Malami Ahmad Khatami ya fadawa masu ibada a Jami’ar Tehran cewa, “Ya kamata a dauki kwakwkwaran mataki akan wadannan Iraniyawa wadanda masu goyon bayan Amurka suka yaudara, sannan hukunci kamar yadda addinin Islama ya tanada.”

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG