A yau laraba masu gabatar da kara suka bayyana irin caji da ake yi ma Wa Lone, da Kyaw Soe Oo, a wata gajeruwar zaman kotu da aka yi a Yangon. Ranar 12 ga watan Disamba ne aka kama ‘yan jaridar biyu bayan da aka zarge su da samun wasu bayanan sirri da wasu ‘yan sanda biyu suka bas u lokacin da suke cin abinci.
Lauyan ‘yan jaridar ya ce alkalin kotun ya ki ya amince da bukatar bada belin ‘yan jaridar, amma yayi alkawarin cewa zai yanke shawara a zaman kotu na gaba, wanda za a yi ranar 23 ga watan nan na Janairu.
‘Yan jaridar sun hadu da iyalan su, haduwa mai cike da ban tausayi bayan zaman kotun kafin a maida su gidan yari.
A wajen kotun kuwa, ‘yan jarida da yawa sanye da bakaken tufafi ne suka yi gangamin nuna goyon bayan su ga Wa Lone da Kyaw Soe Oo, wasun su na dauke da allunan rubutu dake cewa “aikin jarida ba laifi bane”.
Facebook Forum