Tayin ganawar da shugaba Moon yayi wa takwaran aikinsa na Koriya ta Arewa, na zuwa ne kwana daya bayan da jami’an diplomasiyya daga kasashen biyu suka yi ganawar farko a hukumance tun bayan wadda suka yi a watan Disambar shekarar 2015.
Shugaban Koriya ta Kudu ya fadawa manema labarai a birnin Seoul cewa, taron kolin da kasashen biyu zasu yi ba wai kawai zaman ganawa ba ne. Moon yace tilas a sami tabbacin samun nasara ko ci gaba kafin ya zauna da shugaba Kim Jong Un.
A lokacin taron kolin da aka yi jiya Talata a kauyen Panmunjon da aka yiwa lakabin “na kwanciyar hankali’, inda babu wasu ayyukan soja a wurin, wanda kuma ya raba Koriya ta Arewa da ta Kudu, Koriya ta Arewa ta amince ta tura wakilanta zuwa wasan motsa jiki na Olympics da za a yi wata mai zuwa a Pyeongchang. Kasashen biyu kuma sun amince su gudanar da shawarwari don rage zaman tankiyar da ake yi tsakanin su.
Facebook Forum