Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Julian Assange ya Zama Dan Kasar Ecuador


Julian Assange
Julian Assange

An ba Julian Assange mutumin da ya kirkiro WikiLeaks, dandalin kwarmato ta hanyar internet, da yake gudun hijira a ofishin jakadancin Ecuador a birnin London na tsawon shekaru biyar, izinin zama dan kasar ta Ecuador, bisa ga cewar ministan harkokin kasashen ketare na kasar jiya alhamis.

Ana ganin wannan a matsayin wani yunkurin da bai cimma nasara ba, na kyale Assange ya fice daga ofishin jakadancin ba tare da ‘yan sandan Birtaniya sun kama shi ba. Hukumomin birnin London sun ki amincewa da butakar da kasar Ecuador ta gabatar na baiwa Assange kariyar diflomasiya, da zai bashi damar fita daga ofishin jakadancin ba tare da an kama shi ba.

Assange dai yana zaune ne a ofishin jakadancin kasar Ecuador dake birnin London tun shekara ta dubu biyu da goma sha biyu karkashin wani salon daurin talala sabili da hana tsare shi dangane da binciken da ake gudanarwa bisa zarginsa da aikata fyade da aka fara shekaru bakwai da suka shige.

Duk da cewa kasar Sweden ta yi watsi da shara’ar, ‘yansandan London sun nace akan cewa zasu cafke shi da zaran ya kuskura yayi yunkurin barin opishin jakadancin na Ecuador.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG