Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hana Shiga Da Abinci Da Magunguna Kisan Kiyashi Ne - Guaido

Shugaban wucin gadi na kasar Venezuela, Juan Guaido a Caracas, Venezuela, 10 ga watan Fabrairu, 2019.
Shugaban wucin gadi na kasar Venezuela, Juan Guaido a Caracas, Venezuela, 10 ga watan Fabrairu, 2019.

Kayan abinci da magunguna da sauran kayan agaji na jibge a sashin Colombia na gadar,  ta yadda wata tanka da wasu manyan motocin daukar kaya biyu ke tsaye a tsakiyar gadar.

Mai yiwuwa, shugabannin Venezuela na aikata abin da ka iya zama “kisan kiyashi” ta wajen hana shigowa da kayan abinci, a cewar shugaban kasar na wucin gadi a jiya Lahadi.

“Gwamnati ta san wadanda ke da hannu a wannan hanin. Wannan babban laifi ne na kuntata ma bil’adama, da kuma sojoji,” a cewar Shugaban wucin gadi Juan Guaido.

Sojojin da ya ke nufi su ne wadanda aka tura wata gadar da ta hada Venezuela da Colombia.

Kayan abinci da magunguna da sauran kayan agaji na jibge a sashin Colombia na gadar, ta yadda wata tanka da wasu manyan motocin daukar kaya biyu ke tsaye a tsakiyar gadar.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya umurci sojojin da su hana shigowa da kayan agajin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG