Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Caccaki China Saboda Kuntata Ma Kabilar Uighur


Wata makarantar Islamiyya a yankin Uighur
Wata makarantar Islamiyya a yankin Uighur

A cigaba da gallaza ma tsirarun jinsi da China ke yi, kasar ta 'yan gurguzu ta yi matukar takura ma 'yan kabilar Uighur masu alaka da Turkiyya, abin da ya janyo nuna bacin rai daga Turkiyya da sauran al'ummomin duniya.

Kasar Turkiyya ta yi kira ga China da ta rufe abin da Turkiyyar ta kira “sansanonin garkame” ‘yan kabilar Uighur kimanin miliyan guda, ta na mai bayyana sansanonin da wani “babban abin kunya ga dan adam.”

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya Hami Aksoy ya fada a wata rubutacciyar takarda jiya Asabar cewa, “Yanzu ba wani boyayyen abu ba ne cewa Turkawan Uighur sama da miliyan guda da ke kasar China, wadanda akan kama su ba bisa ka’aida ba, kan fuskanci tsanani, kuma akan jirkita masu hankali a siyasance a sansanonin da aka garkame su da kuma gidajen yari.”

Wannan kalaman na Turkiyya ya biyo bayan labarin mutuwar wani fitaccen marubuci kuma mawaki dan kabilar Uighur mai suna Abdureihim Heyit, wanda aka tsare shi a daya daga cikin sansanonin a lardin Xinjiang a kasar ta China.

Kafar labarai ta Associated Press ta ce ba a iya tabbatar da labarin mutuwar ta Heyit ta wajen wata kafa ta dabam ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG