Firayin ministan kasar Indiya Narendra Modi ya yi alkawarin daukar kwakkwaran matakin maida martani akan mummunan harin da aka kai kan jami’an tsaro a yankin Kashmir dake India, yayinda Indiyar ta ce tana da kwakwarar hujja Pakistan na da hannu dumu-dumu a harin da aka kai, kuma kasar ta nemi sauran kasashe su maida Pakistan saniyar ware.
Bayan da ya gana da masu bashi shawara ta fannin tsaro yau Jumma’a, Modi ya yi alkawarin cewa duk wadanda suka kai harin zasu dandana kudarsu, ya kuma ce za a ba jami’an tsaro damar daukar mataki akan ‘yan ta’addan.
Kungiyar mayakan da ake kira Jaish-e-Mohammad, wadda mazaunin ta ke Pakistan, ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken na mota wanda ya auna wani ayarin jami’an soja jiya Alhamis har sojoji 40 suka mutu, wannan shine hari mafi muni da aka taba gani a yankin cikin shekaru da dama da suka wuce.
Facebook Forum