Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Samamen EFCC: Bafarawa Ya Mayar Da Martani


Alhaji Attahiru Bafarawa
Alhaji Attahiru Bafarawa

A martaninsa ga samamen da jami'an Hukumar Yaki Da Almundahana ta EFCC ta kai gidansa, tsohon gwamnan jahar Sakkwato, ya ce abotansa da Sambo Dasuki ya zarce batun kwangila, wadda bai ma taba karba daga gareshi ba.

Bayan samamen da hukumar yaki da almundahana ta EFCC ta kai gidan tsohon gwamnan jahar Sakkwato Alhaji Attahiru Bafarawa, wanda har yanzu ya ke kasar Saudiyya, tsohon gwamnan ya nuna bacin ransa da kai samamen. Y ace ya kai matsayin da ba zai gudu daga Najeriya don wani zargin da bai da tushe ma ba.

A hirarsa da abokin aikinmu Mahmud Lalo, Bafarawa y ace shi babu abin da zai raba shi da tsohon Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaro Sambo Dasuki, saboda abotansu ba yau ya samo asali ba, tun sun a yara ne. Y ace matukar ya na Najeriya to lashakka zai raka Sambo Dasuki zuwa kotu.

Tsohon gwamnan, wanda y ace shi baba wata kwangilar da aka bas hi, y ace da yadda Allah zai koma gida kwanan nan, saboda ya kusa kammala abin da ya kai shi Saudiyyar.

Ga cikakkiyar hirar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG