Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dasuki da Lauyoyinsa Zasu Koma Kotu Ranar Litinin - Ahmed Raji


 Kanar Mohammed Sambo Dasuki mai ritaya
Kanar Mohammed Sambo Dasuki mai ritaya

Lauyan Sambo Dasuki ya zanta da Muryar Amurka inda ya fada cewa zasu koma kotu ranar Litinin mai zuwa saboda jami'an tsaro sun hana shi Dasukin zuwa kasar waje ya kula da lafiyar jikinsa kamar yadda kotu ta bashi izinin yi.

Akan abun dake faruwa da shi Sambo Dasuki Barrister Ahmed Raji yace zasu koma kotu ranar Litinin mai zuwa domin ta yi nazari akan hanashi tafiya kasar waje ya kula da lafiyar jikinsa.

Yace tun can farko kotun ta bashi izinin ya fita daga kasar zuwa inda zai samu magani. To saidai jami'an tsaro sun hanashi fita.

Akan samame da ake kaiwa gidan Dasuki yace tunanensu a nan shi ne lamarin nada nasaba da rahoton da aka ce wani kwamiti ya bayar inda shugaban kasa ya bada umurnin a kama duk wadanda aka ambaci sunayensu a cikin rahoton.

Barrister Raji yace a tasu fahimtar wannan umurnin bai shafi Dasuki ba domin dama yana fuskantar tuhuma a kotu. Idan akwai wata magana kuma sai gwamnati ta kara wannan sabuwar maganar akan ta kana a cigaba da yin shari'a. Yace watakila umurnin ya shafi wadanda ba'a riga an gurfanar dasu a kowane kotu ba ne. A tasu fahimtar sake kama Dasuki bai ma taso ba.

Dangane da cewa wai jami'an tsaro sun kewaye gidan Dasukin, Barrister Raji yace ba haka ba ne illa dai 'yansandan fararen kaya wato SSS sun sa ido kan gidan su san wanda yake shiga ko fita. Amma babu wani sabon matakin killace gidan. Babu canji akan abun dake faruwa a gidanshi yau da kwanaki goma da suka gabata. Yace saboda haka ba gaskiya ba ne jami'an tsaro sun killace gidansa.

Akan manufar shi Sambo Dasuki Barrister Raji yace abun da yake son cimma shi ne ya wanke sunansa daga zargin almundahana da aka yi masa. Yana son a yi mashi shari'a da adalci domin duk duniya ta gani an yi hakan.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

XS
SM
MD
LG