Kungiyar Tarayyar tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, ta ce zata tura sojoji zuwa Mali da Guinea-Bissau domin sanya idanu kan yadda za a mayar da kasashen biyu turbar mulkin farar hula bayan juye-juyen mulki.
A wurin wani taron koli na musamman alhamis a kasar Ivory Coast, kungiyar ECOWAS ta ce ya kamata kasashen biyu su shirya gudanar da zabubbukan majalisun kasa da na shugabanni a cikin shekara daya. Ta yi barazanar kafa takunkumi idan har shugabannin juyin mulkin suka yi kokarin makalewa a kan mulki.
Kafofin yada labarai sun ambaci jami’an da ba a bayyana sunayensu ba su na fadin cewa za a tura sojojin ECOWAS har dubu 3 zuwa kasar Mali, inda a watan da ya shige sojoji suka yi bore suka hambarar da shugaban kasar da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya.
Ana sa ran tura sojoji kimanin 600 zuwa kasar Guinea-Bissau, inda sojoji suka kwaci mulki ranar 12 ga watan Afrilu, makonni kadan kafin a gudanar da zaben fitar da gwani na shugaban kasa.