Kungiyar Tarayyar tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, ta fada jiya alhamis cewa a shirye take ta girka sojojinta a Mali, inda wasu gungun sojoji suka hambarar da halaltacciyar gwamnatin farar hula a watan Maris.
Shugaban majalisar zartaswar ECOWAS, Kadre Desire Ouedraogo, yace kungiyar tana aniyar tura sojoji da zarar hukumomin Mali sun bukaci tura su.
Ouedraogo ya bayyana wannan da maraicen alhamis a bayan tattaunawar sirri da aka yi ta tsawon sa’o’i da dama a Dakar, babban birnin Senegal, da nufin warware daurin gwarman siyasa a kasashen Mali da Guinea-Bissau bayan juye-juyen mulkin soja.
Shugabannin yankin sun fada cewa ba zasu kyale sojoji su nuna iko kan al’umma a kowace kasa a yankin Afirka ta Yamma ba.
Shugabannin sun bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Mali dake karkashin jagorancin shugaban riko Dioncounda Traore, ta tsara shirin gudanar da zabe, sun kuma bayar da shawarar a maido da majalisar dokokin kasar Guinea-Bissau ta ci gaba da aikinta.
Har ila yau sun yi kiran da a girka rundunar sojojin kasashen yanki a Guinea-Bissau domin sanya idanu kan janye dakarun tallafi na kasar Angola dake can da tabbatar da tsaron shirin maida mulki hannun farar hula tare da taimakawa wajen yin garambawul ga bangaren tsaron kasar.
Kungiyar ta ECOWAS ta yi marhabin da sako tsohon firayim ministan Guinea-Bissau, Carlos Gomez Junior wanda ya zo na daya a zagayen farko na zaben shugaban kasa, da kuma hambararren shugaban riko Raimundo Pereira, wadanda sojoji suka kama a lokacin juyin mulki na watan jiya. Amma kuma ECOWAs ta bukaci da a saki dukkan mutanen da aka kama ana tsare da su ta hanyoyin da suka saba doka a kasar.