Shugaban rikon kwaryar kasar Mali sun kafa sabuwar gwamnati, wata bayan da sojojin suka yiwa shugaban kasar juyin mulki.
Wata sanarwar hadi gwiwa da aka gabatar Alhamis, shugaban riko da Prime Ministan wucin gadi sunce za'a baiwa rundunar soja mukamai uku a sabuwar gwamnati, Ma'aikar tsaro da tsaron cikin gida da kuma ma'aikatar harkokin cikin gida.
Sauran mukamai ashirin da hudu farar hula za'a baiwa.
Idan dai ba'a mance ba bijajjarun sojoji ne suka kwace mulki a ranar ashirin da bakwai ga watan Maris, suka zargi tsohon shugaba Amadou Toumani Toure da laifin kasa baiwa rundunar soja isashen makaman tinkarar tawayen Azbinawa a arewacin kasar
A bayan da kungiyar habakar tattalin arziikin Afrika ta yamma ECOWAS a takaice ta matsawa shugabanin mulkin soja lamba ne, suka yarda su kafa gwamnatin wucin gadi wadda zata shirya zabe.