Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi Allah wadai da juyin mulki da sojoji suka yi a Guinea Bissau, kuma tayi barazanar majalisar zata dauki karin matakan ladabatarwa kan kasar dake Afirka ta yamma.
A jiya Asabar, majalisar ta bukaci a sake maido da abinda ta kira “halattacciyar gwamnatin Guinea Bissau”.
A cikin wata sanarwa da jakadiyar Amurka Susan Rice ta karanta, kwamitin yayi barazanar azawa shugabannin wucin gadi na kasar takunkumi.
A shirye kwamitin sulhun yake yayi nazarin daukar karin matakai na takunkumi da aka auna kan wadanda suka ayyana juyin mulki da ‘yan barandansu, muddin ba’a samu canji cikin lamarin ba.
Sojojin kasar sunyi juyin mulki ne ranar 12 ga watan Afrilu, a dai dai lokacinda kasar take shirin yin zaben shugaban kasa da zai maye gurbin shugaban kasar Malam Bacai Sanha, wadda ya rasu cikin watan janairu.
Jim kadan bayan juyin mulkin ne kuma sojojin suka kama shugaban wucin gadi na kasar, Raimundo Pereira, da kuma mutuminda yake kan gaba a zabenda za’a yi Carlos Gomez, jr. Sojojin basu bada wani dalilinda yasa aka tsare sub a.
Ranar Alhamis sojojin suka nada tsohon dan takarar shugaban kasa Manuel Serifo Nhamadjo, ya jagoranci gwanatin wucin gadi na kasar. Amma jiya Asabar yaki karbar nadin, yana mai cewa,sai majalisar dokokin kasar ce kadai take da ikon warware rikicin.
Tunda farko cikin makon jiya ministan harkokin wajen kasar, Mamadu Jalo Pires yayi kira ga kwamitin sulhun d a ya aike da sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Guinea har sai an warware rikicin kasar.