Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da karuwar ta'addanci a arewacin kasar Mali


Mayakan Asbinawa a arewacin Mali
Mayakan Asbinawa a arewacin Mali

Kwamatin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana Takaici, da damuwar

Kwamatin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana Takaici, da damuwar ganin yadda ayyukan ta’addanci ke dada karuwa a Arewacin kasar Mali, kuma hakan na yin barazana ga zaman lafiyar al’ummar yankin.

An kuma hakikance akwai hannun al-qaida masu ra’ayin rikau a yankin Maghrib dake yin tururuwa zuwa yankin, abinda har yasa ‘yan tawayen samun kwarin gwiwar kame mafi yawan garuruwan dake yankin Arewacin Mali.Wata sanarawar ta fito daga zauren kwamatin sulhun Majalisar Dinkin Duniya na dauke da bukatar janyewar mayakan ‘yan tawaye daga yankin Arewacin Mali domin har an fara samun matsalar karya hakkokin Bil Adama da karancin kayan abinchi a Mali.

A halin da ake ciki, Amurka ta yaba da matakin da kungiyar cinikayya da hadin kasashen Afirka ta yamma (ECOWAS) ta dauka na kokarta shirya yarjejeniya da shugabannin Gwamnatin mulkin sojin kasar Mali da har aka kai ga kokarta maida mulkin hannun farar hula. Mai Magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen Amurka Victoria Nuland tace wannan mataki na ECOAWS abin a yaba da shine sannan ta kara da cewa:

"akwai bukatar ganin an maido da mulkin farar hula a kasar Mali domin hakan ya taimaka tare da baiwa Abzinawa kwarin gwiwar ganin an dauki hanyar kaiwa ga warware matsalolin da suke fuskanta a kasar Mali ba tare da neman ballewa ba.Kuma hakan ne zai taimaka a kaucewa tsoma hannun kungiyar al-qaida dake neman wargaza shirin zaman lafiya."

XS
SM
MD
LG