Majalisar dokokin tace ta kafa dokar domin dakile matsalar dake son zama ruwan dare gama gari a jihar. Kafin wannan sabuwar dokar a kan daure masu laifin aikata fyade daga shekara takwas zuwa goma sha hudu.
Kakakin majalisar dokokin Neja Adamu Usman ya bayyana dalilin da ya sa suka kafa dokar da hukuncin shekara 21. Yace wanda yayi fyade da wanda ya taimaka da wanda ya bada kwayar maye domin fyaden kowannensu sai an yi masa daurin shekara 21.
Shugaban kwamitin shari'a na majalisar Isa Kawu yace matsalar mata ne ya sa suka kafa dokar. Yace matsala ce da yakamata a dauketa da tunane mai zurfi saboda yadda ake wulakantar da mata.
Wata 'yar majalisar dokokin Jummai Jafaru tace daurin shekaru 21 ba zai biya matar da aka yiwa fyaden ba domin an lalata rayuwarta amma zai taimaki masu tsoron Allah.
Tuni dai kungiyoyin mata suka yi maraba da sabuwar dokar. Mary Jalingo shugaban mata 'yan jarida ta yabawa majalisar amma ta kira mahukunta su tabbatar sun aiwatar da dokar idan ba haka ba za'a samu matsala.
Hajiya Mairo Muhammed ita ce ta wakilci kungiyar mata lauyoyi a zaman majalisar tace sun yi murna domin abun da suka dade suna nema ne.