Hare-haren sun lakume rayuka da dama kuma miliyoyin dukiyoyi suka salwanta. Yanzu maimakon lamarin ya fara lafawa sai ma karuwa ya keyi. Kungiyar fararen hula ta matasa mai farautar 'yan Boko Haram ko Civilian JTF tace lokaci yayi da za'a sake salo a nemi masalaha da kungiyar Boko Haram. A bi hanyar laluma da sasantawa domin a kawo zaman lafiya.
Barrister Jibril Gundi mai ba kungiyar shawara ya bayyana dalilin da ya sa kungiyar ta kira a nemi teburin shawara.Ya kira gwamnatin tarayya a zauna bisa gaskiya a yi sulhu. Yace a tabbatar ma kowa babu abun da zai sami kowa domin a fito fili a tattauna a cimma sulhu. Yace su kungiyar Civilian JTF a shirye suke. Yace kwamitocin Turaki da na Nur Alkali duk sun yi batun yin sulhu kuma sun bada hanyoyin da za'a bi. A nunawa mutanen cewa batun sulhun da gaske a keyi babu yaudara ciki.
Dama kungiyar Civilian JTF ta fito ne domin ta tabbatar babu wanda aka cuta amma a kawo zaman lafiya. Abun da ya fi mahimmanci wurin kungiyar shi ne kaiga zaman lafiya ko yaya.
Ita ma kungiyar daliban makaranta gaba da sakandare ta jawo hankalin shugaban kasa kan irin abubuwan dake faruwa a arewa maso gabas musamman a jihar Borno. Shugaban kungiyar a jihar Borno Mohammed Isa Biu yace su yanzu kwanciyar hankali suke nema. Sabili da haka suna kiran shugaban kasa ya ziyarci Borno ya gani da idanunsa abubuwan dake faruwa. Idan ba zai iya zuwa ba to ya turo wakilinsa. Ya zo domin ya san dalilin da gwamna Shettima ya yi furunci da gwamnatin tarayya tace ya bata mata rai. Mohammed Isa Biu yace ba laifin gwamnan ba ne domin abubuwan sun fi karfinsa. Shekara da shekaru ke nan ana kan abu daya.