Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanarda Zaben Kananan Hukumomi a Jihar Filato Cikin Kwanciyar Hankali


Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang
Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang

Bayan an dade ana ta daga zaben kananan hukumomi a jihar Filato yanzu dai an yi zaben amma banda kananan hukumomi biyu.

Cikin tsauraran matakan tsaro aka yi zaben kananan hukumomi goma sha biyar cikin goma sha bakwai a jihar Filato.

Banda bada hutu da gwamnatin jihar ta yi tun wajen karfe shida na safiyar jiya rundunar tsaro ta girke jami'an tsaro a koina cikin jihar domin dakile kowane irin tashin hankali da ka so ya kunno kai lokacin zaben.

Mutane sun fito rumfunan zaben inda suka yi layi domin jefa kuri'unsu. Masu zaben sun shaida cewa lamarin na tafiya daidai, babu wata matsala. Wata Mary Peter da take kan layin zaben ta ce tun da safe wajejen karfe bakwai da aka fara babu wata hayaniya. Shaidu sun ce an kawo kayan aiki bisa kan lokaci.

Shugaban hukumar zaben jihar Peter Dalyop yace ya zagaya ya gani da idanusa abubuwan dake faruwa. Ya tabbatar cewa zabe yana gudana ba tare da wata tangarda ba. Yace ba'a taba yin zabe cikin kwanciyar hankali ba irin na wannan karon. Yace ya kamata su yabi gwamnansu Jonah Jang domin ya shirya zabe mai inganci.

Amma a yankin Pankshin matasa sun hana yin zabe domin rashin kayan aiki. Jami'an zaben sun ce sai daga baya ne za'a kawo kayan aiki lamarin da matasan ke ganin wani shiri ne na kokarin tafka magudi.

Shugaban hukumar zaben ta jihar Mr. Peter Dalyop yace an raba kayan aiki a yankuna uku domin a kai kayan aiki a koina kan lokaci. To saidai yace sun samu korafe-korafe daga wasu kan cewa basu ga sunayensu ba. Shugaban yace sun nuna masu cewa basu ba ne ke yin ragistan sunayen mutane. Aikin INEC ne. Su ma sun ara ne su yi anfani da shi. Yace basu da izinin su yi ragistan masu zabe. Amma kan kayan zabe yace akwai wadanda suke zagawa idan akwai karancin kayan aiki zasu kara masu.

Dangane da wa'adin karfe uku na kammala zaben shugaban yace muddin akwai mutane bisa layi suna jiran su kada kuri'a za'a cigaba har sai an gama.

Kan dakatar da yin zabe a Jos ta Arewa da Wase Alhaji Tijani Musawa yace gaskiya basu ji dadi ba domin sun so a ce an yi zaben dasu saboda wai a yanzu zaman lafiya ya dawo Jos. Ana cigaba da harkokin yau da kullum kuma babu wanda yake tsangwamar wani. Yace da Kirista da Musulmi sun zama daya. Yace sun gane cewa lallai dole ne su zauna tare cikin lumana.

Ita kuma kwamishanar watsa labarai ta jihar Olivia Dazem ta bayyana irin kokarin da gwamnati ta yi domin wayarda kawunan jama'a domin a gudanarda zaben cikin kwanciyar hankali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG