Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Mauludin Kasa da Kasa a Karar Iseyin Jihar Oyo


Musulmaina yin sallah
Musulmaina yin sallah

An kamala taron Muludi na kasa da kasa da aka yi a karar Iseyin Jihar Oyo

An rufe Mauludin kasa da kasa a Karar Iseyin cikin jihar Oyo.

Shehun malami Muhammed Bello Bode Sadu daga jihar Kwara na cikin wadanda suka halarci Mauludin. Yace falalar Mauludi ya kunshi abubuwa uku ne wato imani da kiyaye zuciya.Lokcin Mauludin malaikai zasu zo kana albarkacin Ubangiji zai sauko. Idan ana Mauludi Allah zai dauke azaba uku.Allah zai sawa gidan albarka. Gidan ba zai yi gobara ba. Allah zai daukewa gidan annoba.

Sheikh Mohammad Sheriff Mahmud daga kasar Algeria ya zo domin yin Mauludin. Shi ma Sheikh Tijani Gombe yayi tsokaci kan wadanda suka ce Mauludi bai dace ba.
Yace yin Mauludi bai kaucewa addinin Musulunci ba. Addinin Musulunci addini ne wayayye. Yace duk wani aikin alheri idan an kirkiroshi addinin musulunci zai karba.

Dangane da cewa wasu sun yi Mauludi tuntuni to ko me ya sa suke yin nasu yanzu sai Sheikh Tijani yace Mauludi bashi da rana. Mauludi ana yinsa ne saboda farin ciki da Manzon Allah saboda haka ana iya yinsa kowane lokaci amma ya fi a yi a cikin watan da aka haifi Manzon Allah.

Maauludi bashi da wani kala. Daya yake a koina domin manufarsa shi ne soyayya ga Manzo Allah da cusa soyayyar juna. Banda haka kowane Musulmi na iya yin Mauludi wato ko namuji ko mace.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG