Maharan sun shiga harabar makarantar ne wajejen karfe tara na safe ranar Talata inda suka kama yanka yara kamar awaki suna kuma bankawa gine-ginen makarantar wuta. Wasu yaran ma 'yan shekaru goma zuwa goma sha biyar suna jefasu cikin wutar da suka haddasa.
Daga karshe yara 29 suka rasa rayukansu yayin da wasu 45 suka ji munanan raunuka. Jiya da yamma gwamnan jihar ta Yobe Alhaji Ibrahim Geidam ya kai ziyara makarantar inda ya yi allawadai da abun da ya gani. Ya jajantawa iyaye da suka rasa 'ya'yansu ya kuma yin addu'a Allah Ya ba wadanda suke asibiti sauki.
Abdullahi Bego mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin yada labarai ya kara haske kan lamarin. Yace suna kan rangadi da gwamnan jihar sai lamarin harin ya kai kunnuwansu sai suka karkata zuwa Buni Yadi inda abun ya faru. Banda rasa rayuka kusan makarantar gaba daya an konata. Gidajen kwana na yara da malamai da azuzuwa da ofisoshi da dakunan kwaji duk da dakin karatu an konesu. Abun takaici ne domin babu wata hujja kowace iri da za'a kai hari a makarantar. Gwamnan da duk jama'a sun yi addu'ar Allah Ya tona asirin wadanda suka aikata ta'asar.
Daga bisani saboda jin tausayi, gwamnan ya bada taimakon nera miliyan dari ga makarantar. Kudin zai taimakawa malaman da suka rasa gidajensu da duk abun da suka mallaka domin su samu sauki kafin a san abun da za'a yi nan gaba.