Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Da Hukuncin Kotun Koli, Kudurina Na Ganin Sabuwar Najeriya Na Nan Daram - Peter Obi


Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi (Hoto: Twitter/Peter Obi)
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi (Hoto: Twitter/Peter Obi)

Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke bai karya masa gwiwa ba a kan ganin an sami sauyi a sabuwar Najeriya.

A ranar Litinin 6 ga watan Nuwamba ne Obi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, kusan makonni biyu bayan da kotun kolin kasar ta tabbatar da nasarar da shugaban kasa Bola Tinubu na jam’iyyar APC ya samu a babban zaben ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023.

Obi, wanda ya soki hukuncin da kotun kolin ta yanke, ya amince da cewa an kawo karshen shari’ar babban zaben da ya gabata.

Dan takarar LP, Peter Obi yayin taron manema labarai (Hoto: Facebook/Peter Obi)
Dan takarar LP, Peter Obi yayin taron manema labarai (Hoto: Facebook/Peter Obi)

Da yake jawabi ga magoya bayansa da aka fi sani da ‘Obidients’ a kafofin sada zumunta musamman ma Twitter, wanda aka sauya sunan zuwa X, tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce gwagwarmayarsu na nan daram.

Duk da cewa Peter Obi, wanda ya yi jawabi ga manema labarai tare da abokin takararsa Datti Baba-Ahmed, bai fito karara ya bayyana ko zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027 ba ko a’a, ya ce kudurinsa na ganin an samu sauyi a Najeriya na nan daram.

Haka kuma, Peter Obi ya yaba da kokari da sadaukarwar da matasan Najeriya da ‘yan Obidients suka yi, yana mai tabbatar musu da cewa wannan tafiyar tasu mafari ne ba karshe ba, kuma ga dukkan alamu, ‘yan Najeriya da ma duniya sun ji muryoyinsu tare da lura da irin kokarin da suka yi a wannan kakar zaben.

Peter Ob
Peter Ob

Peter Obi da takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun kalubalanci nasarar da Tinubu ya samu a zaben da ya gabata har zuwa kotun koli.

Atiku da Obi basu gamsu da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa wato PEPT ta yanke a farkon watan Satumba ba, sai suka tunkari kotun koli suna neman a soke zaben Tinubu, a kan dalilan da suka sa aka gabatar da mataimakin shugaban Kashim Shattima sau biyu a takara dabam dabam, da mika takardar shaidar kamalla karatun Tinubu ta bogi, da rashin wallafa sakamakon zabe ta yanar gizo, da kuma rashin samun kaso 25 cikin 100 na kuri'u a babban birnin tarayya Abuja, da dai sauransu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG