Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Da Ci Gaban Da Aka Samu, Nahiyar Afirka Na Fuskantar Barazana Daga Kungiyar IS - MDD


Wani ‘dan kungiyar IS
Wani ‘dan kungiyar IS

Nahiyar Afirka har yanzu na ci gaba da Fuskantar barazana daga Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini ta IS yayin da ake fama da tashe-tashen hankula na siyasa a yammacin Afirka da yankin Sahel.

WASHINGTON, D. C. - Kungiyar kuma har yanzu tana da niyyar kai hare-hare a kasashen waje, in ji jami'in yaki da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a jiya Alhamis.

Vladimir Voronkov ya sake nanata binciken da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na cewa kungiyar IS na ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, musamman a yankunan da ake fama da rikici, duk kuwa da gagarumin ci gaba da kasashe mambobin MDD suka samu wajen tunkarar wannan barazana. Voronkov ya ce kungiyar ta kuma kara kai hare-hare a tsoffin tungar ta Iraki da Siriya da kuma kudu maso gabashin Asiya.

Voronkov ya shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, lamarin ya tabarbare a yammacin Afirka da Sahel, “kuma yana kara sarkakewa,” yayin da rikicin kabilanci da na yanki ya shiga cikin ajanda da ayyukan kungiyar masu tsattsauran ra’ayi. , wanda kuma aka fi sani da sunansa na Larabci, Daesh, da masu alaka da shi.

Ya kara da cewa, masu alaka da 'yan ta'addar Daesh suna ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da samun 'yancin cin gashin kansu daga cikin kungiyar ta Daesh, yana mai gargadin cewa idan har aka ci gaba da yin hakan akwai hatsari "babban yanki na iya fuskantan rashin zaman lafiya daga kasar Mali zuwa kan iyakokin Najeriya."

Sojojin Iraqi
Sojojin Iraqi

Natalia Gherman, babban darektan kwamitin zartarwa na kwamitin yaki da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya, ta ce: "Suna amfani da rashin zaman lafiya don fadada tasirinsu, da ayyukansu akan yankunan Sahel, tare da kara nuna damuwa ga gabar tekun yammacin Afirka."

"Nahiyar Afirka yanzu ta kai kusan rabin adadin ayyukan ta'addanci na duniya, inda tsakiyar Sahel ke da kashi 25% na irin wadannan hare-hare," kamar yadda ta shaida wa majalisar.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG