Tallace-tallace dai a arewacin Nijeriya ba wani sabon abu bane ba, domin mafi akasarin kananan yara mata da basa samun damar zuwa neman ilimi na dogara ne akan sana’ar tallace tallace, wadanda mafiyawa ke faraway daga hannun iyayen riko wani wani lokacin ma a wajen iyayensu na ainihi.
Ita dai wannan yarinya mai kimanin shekaru 16, daga karmar Hukumar Kumbotso ta samu ciki ne bayan wani matashi da ya sayi gyadar da take talla ya kuma bukaci da ta bishi daki domin karbar kudinta, inda a nan ne ya afka mata.
Wannan yarinya dai ta ce tana gudanar da tallar gyada ne a lunguna daban daban, domin nemawa wadda ke rike da ita kudin shiga.
Akan haka ne muka tuntubi kwamanda hukumar hisbah na jihar kano, Mal Aminu Daurawa inda ya bayya cewa wannan lamari yana nuna illar dorawa yara kananan talla, ya kuma kara da cewar baya haifar da da mai ido sai nadama da bakin ciki.
Wata mai rajin kare hakkin mata, Barista Badiha Abdullahi Mu’az, ta bayyana abubuwan da ke haddasa yawan fyade tare da hanyar da za’a magance fyade a cikin al’umma.
Baristar Badiha dai ta ce fyade karuwa yake a yanzu, inda ta ja hankalin al’umma da cewa ya zama wajibi a hada hannu wajen tarbiyantar da al’umma gudun abinda `ka iya faruwa nan gaba.