A shirinmu na nishadi, yau mun canza salo domin kuwa mun yi duba ne akan fim din Dan Birni domin sauya tunanin mai sauraronmu.
Film din Dan-birni, fim ne da ya zo da wani salo sabanin sauran galibin fina-finan da aka saba gani a masana’antar Kanywood, inda marubucin ya yi kokarin sauya tunanin masu kallo ta hanyar fito da kalubalen da malam Bahuashe ke fuskanta, musssamman ma dangane da karbar digon allurar riga kafin cutar shan inna wato POLIO.
A zantawarmu da marubuci kuma mai bada umarni na wannan Fim, wato Falalu A Dorayi, ya yi bayani filla-filla game da dalilan kirkiro Fim din, da kuma sakonnin da ke kunshe a cikinsa.
Kamar yadda mai bada umarni ke cewa, malam Bahaushe a da yana zaton ana samun cutar shan inna ne sanadiyar wata aljana da ke shafar mutum.
Mai bada urmannin ya yi karin haske kan yadda fim din ya nuna hanyar da mutum zai bi, domin kare kai daga kamuwa da cutar shan-inna.
Daga karshe dai Falalu Dorayi ya ce sun samu biyan bukata, tunda sun isar da sakon da ke nuna muhimmancin digon rigakafin shan-inna.
Saurari cikakkiyar hirar a nan.