Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Kwallon Kafa Ta Maza Da Ta Mata Sun Yi Bore A Jihar Taraba


Zanga Zangar Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Jihar Taraba
Zanga Zangar Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Jihar Taraba

Wannan ne dai kusan karo na uku da ‘yan kungiyar kwallon kafa ta jihar Taraba, watoTaraba Football Club ,da kuma takwarorinsu na mata,Taraba Queens ke nuna fushinsu game da batun rashin biyansu albashi na tsawon watanni 21.

Su dai ‘yan kungiyar biyu sun gudanar da zanga-zangar lumana ne a kofar shiga gidan gwamnatin jihar Taraban dake garin Jalingo, kuma da yake bayyana dalilansu na wannan zanga-zangar lumanar, mataimakin jagoran yan wasan (Assistant Captain) Uzih Micheal ya zargi gwamnatin jihar da nuna musu shakulatin bangaro.

‘’Wannan ne yasa muka gudanar da wannan bore, domin mun gaji da wannan wulakancin da gwamnatin Taraba ke nuna mana.

‘’Yanzu haka watanni 21, ke nan ba’a biya mu albashinmu ba, don ko a shekarar 2015, sun rike mana albashin watanni 10, haka nan kuma akwai watanni 11, a wannan shekara ta 2016.

‘’Ko a watan Nuwamba mun gudanar da irin wannan zanga-zangar a nan, kuma an yi alkawarin za’a biya mu kafin karshen watan, to amma har zuwa yanzu ba mu ga koda kwandala ba, a cewarsa.

Micheal yace kungiyarsu a baya tana cikin jerin kungiyoyin dake Firimiya league, a shekarar 2014, to amma suka rikito zuwa ajin Pro-League, sakamakon yunwar da suke fama da ita, biyo bayan rashin biyansu hakkokinsu da gwamnatin jihar ke yi.

Shima wani dan wasan Kabiru Ahmed cewa yayi, ‘’ ba zamu bar wannan bore ba sai an biya mu hakkokin mu”.

‘’Ai abun takaici ne, gwamnati ta ki biyanmu to amma gashi ta ware makudan miliyoyin naira wajen shirya baje kolin rawa, wato peace concert, mu ba zamu amince ba,’’ in ji shi.

Jami’an tsaro dai sun yi kokarin su tarwatsa su ta hanyar amfani da barkwanon tsohuwa to amma suka jajirce.

Kokarin ji daga bakin kwamishinan harkokin wasannin jihar Fasto Gambo Ude Indafo, ya ci tura, to sai dai kuma hadimin gwamnan ta fuskacin harkokin yada Labarai Mr Sylvanus Giwa, yace gwamna Darius Dickson Isiyaku, ya yi alkawarin za’a biya yan wasan kafin nan da kristimeti.

‘’Don haka su kwantar da hankulansu,ba a mance da su ba,’’inji shi.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG