Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Facebook Messenger: Mutane 50 Zasu Iya Kiran Juna Ta Bidiyo A Lokaci Guda


Kamfanin Facebook ya sanar da cewa ya kara karfin manhajarsa ta aikawa da sakon karta kwana mai suna Messenger app, wadda mutane kamar 50 zasu iya yin wayar bidiyo a lokaci ‘daya.

Mutane shida na farko dake yin wayar zasu iya ganin junansu kan allon waya ko kwamfutar su, idan mutanen suka wuce shida to duk wadanda suka fi yin magana hotunansu ne zasu kasance kan allunan.

Yanzu haka dai wannan fasahar ta manhajar Messenger app ta doke sauran kafafen sadarwa na kiran wayar bidiyo kamar su Google Hangout da Skype wadanda cikinsu mutane goma ne kadai zasu iya kiran wayar bidiyo.

Facebook dai na kokarin ganin ya janyo hankalin mutanen dake mu’amula da hotunan bidiyo baki ‘daya, wanda a baya bayan nan ne kamfanin ya fitar da wata sabuwar manhajar da ma’aikata da ‘yan kasuwa zasu rika amfani da ita don bunkasa kasuwancinsu.

Duk masu amfani da manhajar Facebook ta kan na’urorinsu da suka hada da Android da ios zasu iya sabunta manjarsu ta yin update.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:01 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG