Kamfanin yada zumunta na Facebook, na wani sabon yunkuri don dakile labarai marasa tushe. Kamfanin dai suna shirin samar da wata hanya mafi sauki, da idan labari bashi da asali bale tushe, su bayyanar da labarin a matsayin labarin kanzon kurege.
Abun da suke kokarin yi shine, idan mutun yaga wani labari da bana gaskiya ba a shafin shi, zai iya amfani da wata dama da suke son kirkira don dannawa, duk wanda ya gani zai san da cewar wannan labari ne da bana gaskiya ba.
Za kuma su hada kai da kamfanonin jaridu kamar su ABC, da Associate Press, kana da wani kamfani mai zaman kanshi dake tantance ingancin labarai “fact-checking website Snopes” Idan mutane suka saka labarai, wadannan kamfanoni zasu taimaka wajen tabbatar da sahihancin labarin.
Idan kuwa labarin bashi da tushe, nan da nan zasu lakamishi alamar cewa labarin shafalabarin shuni ne. Haka kuma idan labarin ya shiga cikin wannan tsarin, babu wanda zai iya kara tura labarin gaba. Kuma babu wata dama da mutane zasu samu wajen bayyanar da sunan wanda ya rubuta labarin.
Gabanin zaben kasar Amurka, da aka gabatar ne a watan da ya gabata, wasu labarai suka bayyana na cewar Fafaroma Francis, yana goyon bayan zababben shugaban kasar Amurka, haka da labarin wani jami’in hukumar binciken manya laifufuka ta FBI mai goyon bayan Uwargida Hillary ya mutu.