Biyo bayan mika sunan dan takarar mataimakin dan takarar shugaban kasa da APC ta yi a boye, masana shari'a na nuna hakan bai sabawa dokar zabe ba matukar wanda a ka mika sunan ya amince da hakan.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Barista Buhari Yusuf ya ce akwai tanadin hakan a sabuwar dokar zabe.
Barista Yusuf ya ce an yi la'akari da rasuwar Abubakar Audu bayan lashe zaben gwamnan Kogi inda a ka yi ta nazarin hanyar warware lamarin da hakan ya sa a ka ba wa jam'iyya hurumin sauya dan takara in wanda ya ke kai ya rasu ko ya ajiye da radin kan sa.
Don haka lauyan ya ce duk lokacin da wanda a ka nada a boyen ya rubuta cewa ya sauka APC za ta iya sauya shi.
Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Abuja Dr.Farouk BB Farouk ya ce APC na daukar matakai masu nuna sai ta kara sauya tsari matukar za ta iya dorewa kan gado a babban zaben 2023.
Hukumar zabe ta rufe karbar sunayen 'yan takarar shugaban kasa daga jumma'ar nan inda yanzu za a jira a ga shin wa za a sauya wa za a bari.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: