Janar Mansur Dan Ali mai ritaya kuma wakili a taron kasa da ake gudanarwa a Abuja ne ya furta haka a wata hira da yayi da muryar Amurka.
Yace “ kada bayan cire dokar tabaci wasu abubuwa su zo suna faruwa za’a ce don an cire ne,amma tun farko ita dokar tabaci ana yi ne a lokaci sojoji ana cire dukan mukamai na wadanda suke rike da jihohi,amma yanzu na siyasa da suka zo sai suka canja aka barsu, kaga abun yana da kala biyu.
Janar Mansur Dan Ali yayi Karin bayani akan nasaran da aka samu dagane da dokar tabaci da aka sa a can baya kamar haka “amfanin da aka samu akai kaga irin ciki garuruwa wanda da Maiduguri bata shiguwa,yau ayi bom nan gobe ayi wancan kaga abubuwan sai aka tura shi baya saboda zaman jami’an a koina,ada ana neman dokar tabaci kafin soja ya bar bariki."