Yanzu masana harkar tsaro suna tambayar yadda aka kashe kudaden da kasar ke ikirarin ta kashe sabili da tsaro. A cikin shekaru hudu alkalumma sun nuna cewa kasar takashe dalar Amurka biliyan ashirin da uku kwatankwacin nera tiriliyon uku da biliyan dari shida.
Manjo Yahaya Shinko mai ritaya yace akwai abun dubawa. Idan ba cin hanci da rashawa ya yiwa kasar katutu ba kowa yana mamakin yadda za'a kashe irin wadannan makudan kudaden kuma ba'a gani a kasa ba. Yakamata a ga alamun hakan daga irin horon da ake ba sojoji da irin makaman da suke anfani da su da kayan aiki da kwarewarsu. Abun mamaki kwarewar 'yan bindigan da makamansu sun fi na sojojin Najeriya.
Wurin tattara bayanai sun fi jami'an tsaron Najeriya. Misali idan sojoji sun bar wani wuri lokacin suke kai hari. To dole a rika zargin cewa shugabannin tsaron Najeriya suna da wata riba da suke ci a tabarbarewar tsaro dalili ke na suka dage sai an kara wa'adin dokar ta baci.
Dangane da abun da ya kamata a yi a kawo karshen matsalar tsaro domin a kubutar da arewa daga durkushewa Dr Bawa Abdullahi Wase yace mafita ita ce wadanda duk aka kamasu inda aka yi rigingimu a yi masu hukuncin kisa. Wadanda suke sayar masu da makamai su ma a yi masu hakan. Matasa suna da yawa da basu da abun yi . Gwamnati ta tanada masu abun yi domin in ba haka ba to duk wanda ya zo shiriya makarkashiya matasa zasu shiga ciki. Duk wadanda aka kama da laifi to dole 'yan Najeriya su san irin hukuncin da aka yi masu domin ya zama kashedi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz